<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Ya Allahna LW547</title>
<lyrics>[V1]
 1)Ya Allahna ina ta yin mamaki
 Kan ayyukan waɗanda kai ka yi
 Ka hallici sammai da dukan duniya
 Kana ta mulkin su ba fasawa.
 KORUS
 Sai dai in shaida daga zuciya
 Babu misalin girmanka.

[V2]
 2)Ka yi magana da tekuna sun taru
 Ka sa ta tsiro da anfaninta
 Ka hallici ɗan Adam cikin duniya
 Ka ba mutum lumfashin hancinsa.
 Korus

[V3]
 3)Amma abin da ya fi ban mamaki
 Shi ne yadda ka ba mu mai fansa
 Ɗanka ya zo ya mutu maimakonmu
 Cikin wannan mugunwar duniya.
 Korus

[V4]
 4)Ran da zan tsaya gaban kursiyinka
 Zan ga dukan ɗaukakar ka
 Zan tuna yadda cikin yawan ƙaunar
 Ka ba mu salamar ka
 Korus</lyrics>
<hymn_number>547</hymn_number>
</song>